Lamarin ya faru ne a kauyen Wiye dake tazarar km 9 ta bangaren kudu maso gabascin garin Bani-Bangou inda ‘yan bindigar da suka zo akan babura suka bude wuta akan wasu fararen hular da suka tarar suna tsakar aiki a gonaki.
Magajin garin Bani-Bangou, Oumarou Bobo ya yi bayani cikin harshen zabarmanci, inda ya ke sanar da wasu makusantansa faruwar wannan mummunan al’amari cikin yanayin damuwa.
"Ina sanar da ku cewa har cikin gonaki ‘yan bindiga suka kai hari inda suka karkashe mutuM 12 a Wiye, cikinsu har da mace 1. Sannan suka wuce zuwa kauyen Dareye-deye inda anan ma suka halaka wasu mutane 2 dake kan amalanke akan hanyarsu zuwa neman ciyawar bisashe wato mutun 14 kenan aka kashe mana a wannan la’asariya. Muna fatan Allah ya jikansu."
Wannan ba shi ne ba ne karon farko da ‘yan bindiga ke kai hari akan fararen hula a gundumar Bani Bangou.
Amma a yadda abin ya rutsa da manoma a gonakinsu ya sa wasu ke kallon abin ta wata fuska ta daban in ji wani mazaunin yankin Tilabery da ya bukaci a boye sunansa saboda dalilai na tsaro.
Ya ce sukan ba manoma tsoro a nan yanki, sun hana su noma kwata-kwata. Addu'an su shine Allah ya ba ma'iakatar tsaro nasara a kan wadannan 'yan bindiga.
Matsalar tsaro a yankin Tilabery wani abu ne dake da matukar sarkakiya sakamakon yadda ‘yan ta’adda suka yi nasarar samin hadin kan wasu daidaikun mutane daga cikin jama’ar dake zaune a wannan yanki yayinda bayanai ke nunin wasu na fakewa da dadediyar gabar dake tsakanin kabilu don tafka ta’asa da sunan ta’addanci.
Masana sun ce matakin sojan da gwamnatin Nijer ta kara tsaurarawa a ‘yan watanin nan ya sa ‘yan bindigar karkatar da aiyukansu zuwa salon kisan fararen hular da ba su ji ba su gani ba yayinda wasu rahotanni ke nunin rashin ganin kanta a fagen daga ya sa wasu mayakan jihadi fara mika makamai a yankin na Tilabery.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: