Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Kama Wani Jigo A Kungiyar Boko Haram


Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya (Facebook/Dakarun Najeriya)
Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya (Facebook/Dakarun Najeriya)

An jima ana neman Modu ruwa a jallo, saboda irin rawar da yake takawa wajen kitsa ayyukan ta’addanci a cewar sojojin Najeriya.

Rundunar “Operation Hadin Kai” da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta yi nasarar cafke wani babban mamba a kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwar da Kakakin sojojin Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu ya fitar ta ce, Yawi Modu ya shiga hannu.

An jima ana neman Modu ruwa a jallo, saboda irin rawar da yake takawa wajen shirya ayyukan ta’addanci a cewar sojojin Najeriya.

“Bayan da muka samu bayanan sirri, mun samu nasarar cafke Yawi Modu, mamba a kungiyar Boko Haram/ISWAP, wanda dama yana cikin jerin sunayen mutanen da ake nema.” Sanarwar ta ce.

Wata motar mayakan Boko Haram da sojoji suka kona (Facebook/Sojojin Najeriya)
Wata motar mayakan Boko Haram da sojoji suka kona (Facebook/Sojojin Najeriya)

Sojojin Najeriyar sun ce sun kama Modu ne a hanyar Dambo-Wajiroko.

Dakarun na Najeriya sun kuma ce sun yi nasarar kwato wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen hada bam din gida a Damboa da ke jihar Borno da kuma Gashua a jihar Yobe.

Kazalika, rundunar ta kuma ce ta yi nasarar gano wani wuri da ake sayar da takin Urea inda daga nan ‘yan ta’adda ke samun kayayyakin hada bama-bamai.

Idan za a iya tunawa gwamnati ta hana sayar da takin na Urea saboda amfani da ake yi da shi wajen hada sinadarin bam.

A ‘yan makonnin nan, dakarun na Najeriya na ba da rahoton cewa mayakan Boko Haram na ta mika wuya saboda nasara da suka ga ana yi akansu.

XS
SM
MD
LG