Dakarun Kamaru na kokarin gano inda aka boye wasu dalibai da shugaban makarantarsu su 81, wadanda aka yi garkuwa da su a makarantar Presbyterian da ke arewa maso yammacin kasar.
Wani gungun ‘yan bindiga da ake kira “Amba Boys” ne ya yi garkuwa da daliban a yankin da ke amfani da harshen Ingilishi, wanda yake ikrarin ya balle ya koma Ambazonia a matsayin kasa mai zaman kanta, inda mayaka ‘yan aware ke jagorar fafutukar.
“Ina so na mika wannan sakon da babbar murya zuwa ga ‘yan ta’adda, mun san cewa sun tunzura mu, suna fyade suna kisan kai suna kwashe kayan jama’a, amma su kwan da sanin cewa za su fuskanci fushin hukuma.” Inji gwamnan yankin Adolphe Lele Lafrique.
Wadanda suka yi garkuwa da daliban makarantar sun ce ba za su saki yaran ba, har sai sun cimma burinsu na samun ‘yancin gashin kansu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga ke garkuwa da dalibai ba, a watan Satumbar da ya gabata, ‘yan awaren sun yi garkuwa da wasu dalibai shida a makarantar kimiyya ta Presbyterian da ke yankin Bafut a kusa da birnin Bamenda, amma daga baya suka sake su bayan da aka biya kudin fansa.
Facebook Forum