Wani babban jami’in gwamnatin kasar Redwan Hussein ya fada wa manema labarai a birnin Addis Ababa a jiya Talata cewa, lamarin ya faru ne a yayin da tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kokarin zuwa sansanin Shemelba na ‘yan gudun hijirar Eritrea.
Ya fadi cewa sojoji sun bude wa jami'an wuta ne a lokacin da suka yi kokarin wuce wani wurin binciken jami’an tsaro na uku. Hussein ya kuma ce an kama jami’an amma tuni aka sako su.
“Mun ga rahotannin da suka bayyana cewa an yi harbi kan tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Tigray, a cewar Stephane Dujarric, mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya a New York. “Wadannan rahotannin abin damuwa ne kuma muna tattaunawa a matakin koli don bayyana damuwarmu da kuma tabbatar da kauce wa aukuwar hakan nan gaba, a cewarsa.