“Za mu zama na karshen ganin harbin kan mai uwa da wabi,” kudurin da Emma Gonzalez ta yi Kenan, wadda ta tsallake rijiya da baya a harbin kan mai uwa da wabin da aka yi a Makarantar Sakandaren Marjory Stoneman Douglas a jahar Florida. Gonzalez ta yi wannan kudurin ne yayin da ta ke magana a wani gangamin kiran a tsai da wanzuwar bindiga a jiya Asabar, kwanaki uku bayan da wani tsohon dalibin makarantar ya bindige ‘yan ajinsu Gonzalez su 17 da kuma wata malama.
Gonzalez ta yi magana gabanta-gadi ga masu sauraronta, wadanda daruruwan mutane ne da su ka taru a harabar kotun tarayya ta Fort Lauderdale, mai tazarar kilomita 45 daga inda harin ya auku.
Gonzalez ta ce matsalar tabin hankali – wadda ita ce Shugaba Donald Trump da sauran hukumomi kan danganta da harbe-harben – ba ita ce babban sanadi ba; ta dora laifin kan rashin tsaurin dokar bindiga ta Florida, wadda a karkashinta ne wannan matashin maharin mai suna Nikolas Cruz ya sayi makaman na shi.
Facebook Forum