Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da PDP da APC na Zargin Juna da Shirya Gadar Zare


Jigajigan siyasar Nijeriya, wadanda a yanzu wasunsu na PDP wasu kuma na APC.
Jigajigan siyasar Nijeriya, wadanda a yanzu wasunsu na PDP wasu kuma na APC.

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya da babbar jam'iyyar adawa ta APC su na zargin juna da shirya ma juna gadar zare.

A yayin da zaben 2015 ke kara matsowa, jam’iyyar PDP da APC na kara zargin juna da shirya gadar zare musamman ma ta wurin dasa mambobin boge wadanda za su rinka kawo fitina cikin jam’iyya. A yayin da APC ke zargin cewa PDP sakawa ‘yan korenta da ta kura su leko asiri da shuka barna a APC da mukamai ko kariya daga hukumar yaki da almundahana ta EFCC, ita kuma jam’iyyar PDP na cewa APC ta yi kwance-kwance ta kwace mata wasu gwamnoni da jigajigan mambonbi.

Furfesa Alkali Ahmed Refu’I mai bai wa Shugaba Jonathan Shawara kan Siyasa ya ce ‘yan APC na zargin Buba Galadima da zama dan koren PDP alhalin su ma sun kwaso gwamnoninsu da Sanatocinsu sun sa a jam’iyyarsu ta APC, wadanda ka iya lalata masu jam’iyya fiye da Buba Galadima.

Shi kuwa wani dan Majalisar Dokoki daga yankin arewa maso gabas da ya canza sheka daga PDP zuwa APC mai suna Umaru Baranbu ya ce ya canza sheka ne saboda kishin kasarsa. Ya musanta zargin cewa ya shiga APC ne don yin aiki ma PDP.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye


TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG