Ga alama dai, Jam’iyyar adawa ta APC a Jihar Neja, na fuskantar zaben fidda gwani, domin fitar da wanda zai nemi zama gwamna a babban zabe mai zuwa.
A yanzu dai jam’iyyar ta APC nada ‘yan takarar neman mukamin gwamna guda hudu. Amma bayanai sun nuna cewa biyu daga cikinsu, da suka fito daga yankin arewacin Jihar, wato Alhaji Habu Sani Bello, da kuma Sanata Ibrahim Musa.
Sanata Ibrahim Musa yana da karfin gwiwar cewa jam’iyyar zata bashi damar yi mata takara, saboda a cewarsa, yana daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar na ainihi.
“Duk wanda yazo, ya same mu ne, wasu sunzo nan ne, saboda sun kasa samun dama a PDP”, a cewar Sanata Ibrahim Musa.
Shi kuwa Alhaji Habu Sani Bello, da aka fi sani da Habu Lolo cewa yayi a yanzu, bashi da masaniyar yin sulhu da wani dan takara.
Mr. Bello ya kara da cewa “ana demokradiyya, kowa yana da ‘yancin ya fito takara, kuma ita jam’iyya tana son cigaba”.
A yanzu dai, lokaci ne zai nuna, yadda wannan kokawa zata kaya.