Amma abu mai daure kai shi ne karar da Farfasa Dupe Abiola tayi a babban kotun tarayya tana bukatar hukumar zabe kada ta bar kowa ma yayi takara a jam'yyar PDP din tunda jam'iyyar ta hanata takardar tsayawa takara.
Amma nan take jam'iyyar PDP tace da gangan ita Farfasa din ta ki zuwa karbar takardar takaran domin neman haddasa fitina.
Mai taimakawa shugaban ta fannin siyasa Farfasa Rufai Ahmed Alkali yace shugaban ya bada dama har ma ranar karshe kafin ya mika takardar takaran domin ba kowa taka rawa.
Farfasa Alkali yace babu wanda aka hanashi sayen takardar tsayawa takara. Ranar karshen sayen takardar 30 ga watan Oktoba ne amma bayan lokacin ya wuce sai da jam'iyyar ta sake bude ranar domin wanda bai sayi takardar ba ya je ya saya.
Sanata Haruna Goje da ya fice daga jam'iyyar PDP yace muddin aka yi zabe mai adalci jam'iyyarsu ta APC zata amshe madafin iko daga PDP ta aiwatar da canjin da zai amfani jama'ar kasar.
Ga karin bayani.