Rahotanni da dumi-duminsu na bayyana cewa gwamnan jihar Cross River da ke kudancin Najeriya Ben Ayade ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya koma APC mai mulkin kasar.
Mamman Mohammed, Babban Daraktan watsa labarai na shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa, kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya tabbatar da cewa gwamnan na jihar Cross River ya jefar da jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC.
Gwamna Ayade ya bayyana matsayar ta shi ne a yau Alhamis, bayan wata ganawar sirri da yayi da wasu gwamnoni 6 da kuma wasu ‘yan majalisar tarayya na jam'iyyar APC da suka ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Calabar.
Gwamnonin da suka kai ziyarar sune na jihohin Kebbi, Imo, Yobe, Plateau, Jigawa da Ekiti.
Mohammed ya ce tuni kuma da Shugaban na APC ya karbi gwamnan na Cross River a hukumance a yau Alhamis.
Gwamna Ayade ya kwashe tsawon lokaci yana takaddama da wasu ‘yan majalisar tarayya da kuma shugabancin jam’iyyar PDP a jihar, akan jayayyar karfin iko da shugabancin jam’iyyar, kazalika da kuma kujerar majalisar dattawa ta Arewacin jihar.
Wannan lamari dai ya haifar da babbar baraka a jam’iyyar ta PDP a jihar.
To sai dai wannan na zuwa ne makwanni 2 bayan da wani kakkarfan kwamitin gwamnonin PDP na sasantawa a karkashin jagorancin gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal suka ziyarci gwamnan na Cross River domin ba shi baki, kasancewarsa daya daga cikin gwamnonin da ke barazanar ficewa daga jam’iyyar.
Yanzu dai hankali ya karkata akan sauran wasu gwamnoni da manyan gimshikan jam’iyyar ta PDP da ke barazanar ficewa, kamar gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle da sauransu, wadanda kuma kwamitin na Aminu Waziri ya ziyarta a can baya domin ba su Magana da sasantawa.