Jam’iyyar PDP da dan takarar ta sun shigar da kara a gaban kotun ne suna kalubalantar sakamakon zaben, wanda ya ayyana gwamna mai ci yazu Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC, a zaman wanda yayi nasara, inda suka bukaci kotun da ta soke sakamakon zaben.
Haka kuma sun bukaci kotu da ta ayyana dan takarar na jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede a zaman wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
To sai dai a hukuncin kotun da ta yanke ta hanyar sadarwar bidiyo na tsawon sa’o’i 2, babban alkalin kotun, mai shari’a Abubakar Umar, ya ce karar ba ta da wani tasiri.
A cewar kotun, “korafe-korafe da hujjojin da PDP ta gabatar a karar, lamurran ne da suka shafi tafiyar da wata jam’iyya da tuni aka sasanta su.”
Akan haka ya ce "kotun ba ta da hurumin bin bahasin wadannan al’amuran."
Tuni dai da jam’iyyar APC ta fitar da sanarwa ta hannun sakatarenta na watsa labarai Alex Kalejaiye, tana mai bayyana gamsuwa da hukuncin kotun.
Jam’iyyar ta yabawa alkalan kotu akan abin da kira “jajircewa bisa gaskiya,” kana kuma ta jinjinawa hukumar zabe ta kasa, akan bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki a zaben.
An gudanar da zaben gwamnan jihar ta Ondo ne a ranar 10 ga watan Oktoban shekara ta 2020, inda hukumar zabe ta bayyana gwamna Rotimi Akeredolu a matsayin wanda yayi nasara a zaben, inda ya kayar da tsohon mataimakinsa Agboola Ajayi da ya yi takara a karkashin jam'iyyar ZLP, da kuma Eyitayo Jegede na jamiyyar PDP.
To sai dai kuma Jegede ya garzaya kotu bayan ayyana shi a zaman wanda ya sha kaye, inda ya bukaci kotu da ta soke sakamakon zaben, ta kuma ayyana shi a zaman wanda ya lashe zaben.
Tuni da aka rantsar da Akeredolu a wa'adin mulkinsa na biyu, tare da mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.