Tun lokacin da cutar ebola ta bullo kai a Najeriya gwamnatin jihar Filato ta dukufa wajen wayar wa al'ummarta kai dangane da cutar.
Ta wayar dasu akan yadda ake kamuwa da cutar da kuma abun da zasu yi su kauce kamuwa da ita. Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Dr Pam Dakwar yace ma'aikatarsa ta horas da ma'aikata wajen dari uku domin shirin ko ta kwana wadanda zasu taimaka wajen bada bayanai da kulawa da wadanda watakila zasu kamu da cutar.
Gwamnatin jihar ta bada nera miliyan casa'in da biyar domin sayen kayan aiki da tanada wuraren da za'a kula da mutane.
Shugaban karamar hukumar Mangu yace zasu bada goyon baya da hadin kan malaman addini da sarakunan gargajiya wajen wayarwa jama'a kai akan illar cutar
Ga rahoton Zainab Babaji.