Sabbin alkaluma daga China sun nuna cewa kashi 75% cikin 100 na adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus amma ba su nuna alamar cutar ba, daga baya alamun sun bayyana.
Maria Van Kerkhove kwararriyar Jami'a a hukumar lafiya ta duniya WHO ce ta bayyana hakan, a wani taron manema labarai a ranar Juma’a a birnin Geneva,
A cewar Kerkhove ana fuskantar kalubale wajen iya gano ko bin diddigin ire-ire mutanen da ba sa nuna wata alama amma daga baya kuma suke nunawa.
Bayanan Kerkhove na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna shakku kan sahihancin alkaluman da China ta bayar dangane da adadin wadanda cutar ta coronavirus ta kama.
Jami’ar ta WHO ta yi kira ga kasashen da cutar ta bulla a yankunansu da su rika fayyace masu dauke da cutar da ba sa nuna alamarta da kuma wadanda ba sa nuna alamar cutar amma kuma daga baya alamunta suke bayyana.
A farkon makon nan ne China ta fitar da alkalumanta a karon farko kan wadanda suka kamu da cutar amma ba sa nuna alamunta inda ta ce za ta fara saka su cikin jerin wadanda suka kamu da cutar.
A baya Chinan ba ta saka sunayen ba, lamarin da ya sa aka gaza samun cikakkun alkaluma kan mutanen da cutar ta COVID-19 ta harba a kasar.
Facebook Forum