Kasar Somaliya ta samu mutum na biyu da ya mutu sanadiyyar cutar coronavirus, wanda hakan ya sa aka kafa dokar hana zirga-zirgar dare a Mogadishu babban birnin kasar.
Kwamandan rundunar ‘yan sandan kasar Janar Abdi Hassan Mohammed, ya ce dokar hana zirga-zirgar zata fara aiki daga ranar 15 ga watan Afrilu da karfe 8:00 na dare zuwa karfe 5:00 na asuba agogon kasar. Sai dai ba a shata lokacin dage dokar ba.
Hukumomi sun kara da cewa dokar takaita zirga-zirgar zata shafi harkokin sufuri da kasuwanci amma baza ta shafi shagunan saida abinci, asibitoci da shagunan sayar da magani ba.
Dokar ta zo ne a ranar da kasar ta sami mutum na biyu da ya mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar COVID-19. Mutumin dai dan majalisar dokoki ne kuma Ministan shari’a a jihar Hirshabelle.
Facebook Forum