Hukumar tsaron Najeriya ta NSCDC ta tura jami’anta 500 zuwa jihohin Adamawa da Taraba, a matsayin martanin gaggawa da kuma gudummuwarta wajen dakile bazuwar annobar cutar coronavirus (COVID-19).
Wannan mataki na amfani da jami'an tsaron farin kaya da suka hada da Civil Defense da ‘Yan sanda, na cikin matakan da hukumomi a yanzu ke dauka a Najeriya na yaki da yaduwar cutar coronavirus.
Nurudden Abdullahi, shine kwamandan rundunar tsaron farin kaya ta Civil defense a jihar Adamawa, ya ce sun tura jami'an su 300 a fadin jihar don tabbatar da an kiyaye dokar zama a gida ko kuma rage cunkuson jama'a kamar yadda gwamnatin Najeriya ta bada umurni.
Ita ma jihar Taraba ta dauki irin wannan matakin, yayin da a bangare guda kungiyoyin ‘yan kasuwa ke ganin akwai bukatar gwamnati ta samar masu tallafi na musamman don ganin halin da ake ciki.
Alhaji Bashir Sambo, na daga cikin shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa dake wannan kiran. Ya ce ya kamata gwamnati ta tallafa wa kananan ‘yan kasuwa saboda wasu daga cikinsu sai sun fita zasu iya samun abinda zasu ci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke ganin akwai bukatar gyara a kalaman da wasu malaman addini ke yi game da wannan annoba ta coronavirus. Dr. Hafiz Sa'id na cibiyar da ake kira Haidar Centre, ya ce ba daidai ba ne wasu su danganta cutar da yi wa wata al'umma makarkashiya.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum