Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Sace Yayan Gwamnan Bauchi


Hukumar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace yayan gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed kauran Bauchi, a unguwar jaki dake cikin garin Bauchi.

Bincike ya nuna cewa wasu mutane dauke da bindigogi ne suka yi dirar mikiya a unguwar da misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba inda suka yi ta harbe-harbe daga nan suka sace yayan gwamnan mai suna Mallam Adamu Muhammed, wanda aka fi sani da yaya Adamu.

DSP Kamal Datti, shine kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi, ya ce sun samu rahoton sace Malam Adamu kuma suna kan binciken gano inda yake tare da kama wadanda suka sace shi.

A gefe guda kuma gwamnatin jihar Bauchi ta umarci wasu rukunan ‘yan kasuwa da su rufe shagunansu, a wani yunkuri na shawo kan yaduwar cutar coronavirus, kamar yadda mukaddashin gwamnan jihar Sanata Baba Tela ya bayyana.

Wasu daga cikin shugabannin ‘yan kasuwa sun yaba da umurnin da gwamnatin jihar ta bayar.

Saurari Karin bayani cikin Sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG