Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Guterres Ya Yi Kira Da a Kawo Karshen Nuna Tsana a Duniya


Antonio Guterres shugaban Majalisar Dinkin Duniya
Antonio Guterres shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce annobar coronavirus ta haddasa tsananin kiyayya da tsanar bakin haure da mayar da juna saniyar ware da kuma baza bayanan tsoratarwa.

Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya baki daya a kawo karshen kalaman kiyayya a fadin duniya.

Cutar mai yaduwa ta yi sanadiyar da shugabannin duniya da ma talakawa suna zargin kungiyoyi a kan barkewar cutar. Sau tari ana kebe bakin haure da ‘yan gudun hijira cewa sune mafarin wannan cutar, har ma akan hana su samun kiwon lafiya, inji Guterres.

Ya ce ana auna ‘yan jarida da masu kwarmato da ma’aikatan kiwon lafiya da na ayyukan ceto da ma ‘yan rajin kare hakkin bil adama a kan suna aikin su.

Babban sakataren na MDD ya ce ana yawan alakanta yawan shekaru da wannan cuta a kan yanar gizo, ana cewa tsofaffi ne suka fi harbuwa.

Shugaban na MDD ya ce yana kira ga kowa a ko ina a fadin duiya da daina irin wadannan kalaman tsana a kiyaye mutuncin juna kana a tausayawa juna.

Akwai kimanin sama da mutane miliyan uku da dubu 800 dake dauke da cutar a fadin duniya kana wasu dubu 259 sun rasa rayukan su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG