Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: China Ta Yi Tayin Kai Wa Afrika Ta Kudu Agaji


Shugaban China Xi Jinping ya ce zai ba kasashen Afirka goyon baya da kuma tallafi, musamman ma kasar Afirka ta Kudu wajen yaki da annobar cutar COVID-19.

Kafafen yada labaran kasar China sun ce a lokacin wata hirar wayar tarho a jiya Laraba da shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, Xi ya bayyana yadda Afrika ta kudu ta yi wa Beijing tayin kai dauki a lokacin da kasar ta fara yaki da cutar coronavirus a karshen shekarar da ta gabata.

Xi ya ce China zata sanar da Afirka ta kudu matakan da suka dauka wajen dakile yaduwar coronavirus kana kasashen biyu zasu inganta hadin kai tsakaninsu a bangaren kiwon lafiya,

Afirka ta kudu tana da sama da mutane 1,800 da suka kamu da cutar coronavirus, adadi mafi yawa a nahiyar. Ya zuwa yanzu an danganta mutuwar mutane 18 da cutar a kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG