Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya gargadi kasashe da karsu siyasantar da annobar Coronavirus wadda ka iya haddasa karin mace-mace, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya soki hukumar tare da barazanar yanke tallafin da ake bata.
Da yake magana kan sukar da aka yi masa a wani taron manema labarai a Geneva, Tedros ya yi kira ga kasashen da su kauce wa siyasantar da annobar “idan har ba a son ci gaba da samun mace-mace.”
Trump, wanda ke shan suka kan rashin gaggauta daukar matakai wajen shawo kan yaduwar annobar a Amurka, ya aike da wani sakon Tweeter ranar Talata mai cewa, “Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi sakaci”.
Sa'anan ya zargi hukumar da zama yar koren China, haka kuma ya ce yana duba yiwuwar yanke tallafin miliyoyin dalolin da Amurka take bai wa WHO.
Facebook Forum