Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Wuce Dubu 403


Adadin mutanen da suka mutu da COVID-19 a fadin duniya ya wuce dubu 403 kana wadanda suka kamu da cutar sun kai miliyan bakwai, a cewar alkalummar da cibiyar nazari ta jami’ar John Hopkins.

Amurka dai na cigaba da zama ta farko wurin da aka fi yawan mace mace sakamakon kamuwa da coronavirus, Birtaniya na biye da ita sannan Brazil da Italiya.

Har iyau Amurka ita keda yawan mutanen da suka kamu da cutar da kusan mutane miliyan biyu sannan Brazil mai kashi uku cikin adadin na Amurka kana Rasha da Birtaniya na biye da su.

A hali da ake ciki an samu wani albishir daga Firai ministan New Zealand Jacinda Arden inda ta sanar a yau Litinin cewa kasar tayi kokari ta dakile yaduwar coronavirus. Kasar New Zealand ta yanke shawarar dage galibin dokokin hana zirga zirga na coronavirus amma kuma zata cigaba da rufe kan iyakokinta.

Sai dai hukumomi a Amurka sun gargadi mutane da shiga cikin zanga zangar kalubalantar mutuwar George Floyd bakar fatar Amurkan nan, da su yi gwajin COVID-19 bayan sama da mako guda da zanga zangar ba tare da nesanta da juna ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG