Yayin da adadin wadanda suka mutu daga cutar coronavirus a Amurka ya haura 5,000, magajin garin Los Angeles ya bukaci mutane a birnin, wanda shine na biyu mafi girma a kasar da su rinka sanya abin rufe fuska idan zasu fita cikin jama'a.
Magajin garin, Eric Garcetti, ya ce ba lalle sai mutane sun yi amfani da abin rufe hanci da baki irin na likitoci ba, da ake da karancin shi yanzu, amma ya ce amfani da kyalle don rufe fuska zai taimaka wajen rage yaduwar cutar.
Har yanzu jami'an kiwon lafiya na Amurka basu bada shawarar mutane su sanya abin rufe fuska ba.
Garcetti ya kuma ce sanya abin rufe fuska ba yana nufin mutane su dinga fita ba ne, ya kamata su zauna gida sai dai in ya zama dole domin wasu muhimman ayyuka, kamar sayen abinci.
Facebook Forum