Jami’ai a jihar Massachusetts dake arewa maso gabashin Amurka, sun ce an sallami shugaban wata cibiyar kula da tsofaffin sojojin Amurka daga aiki, bayan da aka sanar ranar Litinin 30 ga watan Maris cewa wasu tsofaffi da ke zaune a cibiyar su 11 sun mutu, ciki har da mutum 5 da aka tabbatar suna dauke da cutar coronavirus.
Jami’an cibiyar kula da tsofaffin sojoji na jihar sun ce har yanzu dai ana jiran sakamakon gwajin akalla mutum 5 wadanda suka mutu a cibiyar sojojin Holyoke, mai tazarar kilomita 140 daga yammacin birnin Boston.
Jami'an sun ce, an ba shugaban cibiyar Bennett Walsh hutun dole kana gwamnan Massachusetts Charlie Baker ya wallafa wani sako ta twitter cewa, jami’an lafiyar al’umma suna gudanar da bincike a cibiyar, da kuma yadda al’amura ke gudana.
Mataimakin sakateren ma’aikatar lafiyar jihar Dan Tsai, a wata sanarwa da ya fitar ya fadi cewa ma’aikatar ta kafa wata runduna ta kwararru a bangaren kiwon lafiya, da masana a harkokin cututtuka da kuma kwararru a harkar gudanar da ayyuka, domin daukar kwararan matakan yaki da annobar COVID-19.
Facebook Forum