Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ruwaito cewa, an sake samun sabbin mutane biyar da ake fargabar sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.
A jiya Asabar kamfanin dillancin labaran na AFP, ya bayyana cewa, jami’an lafiya sun gano karin mutane biyu a yankin Wangata da kuma wasu mutane uku a yankin Bikoro, duk a arewa maso yammcin Lardin Eqauteur.
Dr. Hiller Manzimbo, darektan babban asibitin yankin na Wangata ya nuna takaic kan yadda har yanzu wasu ba su fahimci cutar ta Ebola ba.
"Har yanzu a nan Mbandaka da kuma watakila Bikoro da sauran wurare, mutane da yawa ba su fahimci cewa lallai akwai cutar ta Ebola ba.” Inji Dr. Manzimbo.
A halin da ake ciki kuma, hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta ce ta dukufa wajen samar da allurar rigakafin cutar ta Ebola.
Allurar wacce ba a tabbatar da ita ba a hukumance, kan samar da kariya, tare da ba da kwarin gwiwar cewa za ta taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Facebook Forum