Nan da makwanni masu zuwa, ana sa ran za a dakile sabuwar barkewar cutar Ebola da ta auku, a cewar kwararrun hukumar Lafiya ta Duniya WHO da kuma na kungiyar likitocin kasa da kasa na Medicine San Frontiers.
Sai dai a wata hira da kwararrun suka yi da Muryar Amurka a wannan makon, sun ce, duk da haka, akwai sauran jan aiki a gaba, yayin da daruruwan ma’aikatan kiwon lafiya na gida da waje ke kokarin yaki da cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.
Amma wata alama da ke nuna haske kan lamarin a cewar Dr. Hilde De Clerck, jami'ar lafiya daga cikin hukumomin, ita ce, an gano asalin wuraren da barkewar cutar ta samo asali a kasar ta Congo.
A baya dai, an yi fargabar yaduwar cutar zuwa sassan yammacin Afirka, kamar yadda aka gani a tsakanin shekarun 2014 da 16, inda mutane sama da mutane dubu 11 suka mutu a kasashen Guinea, Liberia, Saliyo, wanda shi ne lamari mafi muni da mutane suka halaka sanadiyar cutar tun da aka gano ta.
Facebook Forum