Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta na kasar Libiya a wata ziyarar da ba sanarwa domin ta gana da sabbin shugabannin kasar, a yayin da mayakan gwamnatin wucin gadin kasar su ka kaddamar da hari kan gyauron tungar tsohon shugaban kasar Moammar Ghadafi.
A yau talata Clinton ta isa birnin Tripoli inda ta yi alkawarin wani sabon taimakon miliyoyin dololi a fannin ilimi da fannin kula da lafiyar mayakan da suka ji ciwo da kuma fannin gudanar da bincike a kan tarihin mutanen da. Haka kuma za a bada kudaden gudanar da aikin gano dubban makamai masu linzamin da ake dorawa a kafada a harba wadanda ba a san iyakar su ba sannan a lalata su don a hana su fadawa hannun ‘yan tawaye.
Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun ce tun da aka fara yakin kasar Libiya ya zuwa yanzu Amurka ta taimaka ma ta da jimlar kudi dola miliyan 135.
A yayin ziyarar ta, ta Clinton ta gana da Frayim Ministan wucin gadi Mahmud Jibril da kuma shugaban Majalisar mulkin wucin gadi, Mustapha Abdel Jalil. Tun bayan barkewar boren da aka yiwa Mr.Ghadafi a cikin watan Fabarairu, Clinton ce ta fara kai ziyarar aiki birnin Tripoli a cikin manya-manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka.
A halin da ake ciki kuma, a yau talata daruruwan mayakan gwamnatin wucin gadin kasar Libiya sun kaddamar da hari kan birnin Sirte, kwana daya bayan sun kama Bani Walid, tunga daya tallin tal da ta rage a hannun magoya bayan Mr.Ghadafi.