Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Halama Za a Fuskanci Matsalar Abinci a Jamahuriyar Nijer


Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.
Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.

Majalisar Dinkin Duniya tace wasu manoma a Niger suna fuskantar matsaloli sosai

Rashin damina mai albarka tasa ba’a samu ba ko kuma ba za’a samu girbi mai albarka a wasu yankunan kasar Niger ba, to amma kungiyoyin bada agaji sunce nazari da aka yi sosai da kuma bayanan da aka samu akan yadda al’amurra suke tasa an inganta hanyoyin rarraba kayayyakin agaji.

Wakilin Muryar Amirka Scott Stearns ya aiko mana da rahoton cewa, Majalisar Dinkin Duniya tace wasu manoma a Niger suna fuskantar matsaloli sosai domin kuwa babu abinda suka girba.

Denise Brown itace darektar shirin samar da wadatar abinci na Majalisar Dinkin Duniya a Niger, tace gwamnatin Niger da wasu kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun damu da karancin kayayyakin abinci a birnin Agadez inda manoma suka fuskanci rashin girbi mai albarka, a sakamakon rashin isashen ruwan sama da kuma kwarin da suka lalata shuke-shuke. Tace yanzu haka akwai wasu iyalai da suke farfadowa daga farin daya faru a baya a yayinda kuma suke tsumayen zuwan wani farin. Ms Brown tace a takaice ba za’a samu girbi mai albarka a kasar Niger ba. A yayinda a wasu yankunan ma sam-sam babu abinda zasu girba.

Kasar Niger tana fuskantar karancin kayayyakin abinci hade da kruwa yawan jama’a.

XS
SM
MD
LG