A gobe lahadi shugabannin wucin gadin kasar Libiya ke shirin ayyana cewa kasar ta samu cikakken ‘yanci, a wani takun share hanyar kaddamar da matakin kafa sabuwar gwamnati.
Jami’an Majalisar Mulkin wucin gadin da ake kira NTC ko CNT a takaice, sun fada a yau asabar cewa a za yi sanarwar ce a Benghazi, birnin gabashin kasar wanda ya zama sansani ko cibiyar gwagwarmayar nuna kin jinin gwamnati.
Rahotannin farko sun ce, a yau asabar majalisar za ta yi sanarwar. Babu wani bayani game da abun da ya sa aka jinkirta har sai gobe.
Haka kuma a yau asabar, frayim ministan wucin gadi Mahmoud Jibril ya fada cewa ya kamata a yi zaben farko a kasar Libiya cikin watanni takwas masu zuwa, inda mutane za su zabi ‘yan majalisar da za su rubutawa kasar sabon kundin tsarin mulki.
A can baya Mr.Jibril ya fada cewa zai yi murabus daga 'yanci ya samu a kasar Libiya. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito shi ya na cewa ranar asabar zai yi murabus. Jibril ya yi magana ne daga kasar Jordan inda ya ke halartar babban taron tattalin arziki na duniya.
A halin yanzu kuma, majalisar mulkin wucin gadin na kokarin tantance lokaci da kuma wurin da za a binne tsohon shugaban kasar Moammar Ghadafi wanda aka kashe ranar alhamis bayan da mayakan juyin juya hali su ka afkawa garin su na Sirte. Gawar Ghadafi na ajiye a kan wata katifa a cikin wani dakin sanyi a wani tsohon kantin sayar da nama a Misrata.
Hoton bidiyon gawar Ghadafi ya nuna hujin harsashi a gefen kan shi ta hagu da kuma wani hujin a tsakiyar kirjin shi.