A yayin da ake ci gaba da samun Karin goyon baya akan gudanar da bincike mai zaman kansa, dangane da asalin annobar coronavirus. China ta fada a yau Litinin cewa wannan yunkurin azarbabi ne kawai.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China Zhao Lijian, ya fada a wani jawabi cewa akasarin kasashen duniya na da yakinin cewar annobar na ci gaba da yaduwa.
A na sa ran wani daftari da kungiyar Tarayyar Turai ta rubuta, zai sami amincewar babban taron hukumar lafiya ta duniya a wannan makon. Wanda shine shugabancin Hukumar Lafiya ta Duniya – W.H.O.
Matakin na neman a yi bincike akan yadda annobar ta soma, da kuma matakan da aka dauka akan ta.
Kasar Australia tana gaba-gaba wajen ganin an gudanar da wannan binciken, minister harkokin wajen kasar Marise Payne yau Litinin ta ce, suna bukatar binciken ya zama na tsakani da Allah, mai zaman kansa, kuma cikakke.
“Muna da cikakken kwarin gwiwa akan bukatar binciken a cewar majalisar zartarwa ta hukumar lafiya ta duniya.”
An sami gano bayyanar cutar coronavirus a karon farko a kasar China a karshen watan Disamba, daga nan ta yadu a fadin duniya, ta kuma kashe mutun fiye da 315,000 kana fiye da mutum miliyan 4 da dubu 700 suka kamu da ita.
Facebook Forum