Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Gwamnatin Hadaka a Isra'ila


Frai Ministan Isra'illa, Benjamin Netanyahu
Frai Ministan Isra'illa, Benjamin Netanyahu

An kafa sabuwar gwamnati a Isra’ila, bayan da aka kwashe sama da shekara guda ba tare da sanin makomar siyasar kasar ba.

Sai dai har yanzu sabuwar gwamnatin hadakar da aka kafa, wacce za a raba mukamai tsakanin bangaren masu neman sauyi da kuma masu matsakaicin, ra’ayi, ba ta kaucewa, takaddamar da ke akwai ba.

A jiya Lahadi, Majalisar Isra’ila, ta amince da sabuwar gwamnatin hadin gwiwar da kuri’a 73 da 46.

Benjamin Netanyahu zai ci gaba da zama Firayim Minista har na tsawon wata 18.

Shi kuma Shugaban babbar jam'iyyar Blue and White, Benny Gantz, zai maye gurbin “fFrayim minista,” bayan wata 18 inda za su canza mukami.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Netanyahu ya ce, "jama'a na son gwamnatin hadin kai, kuma ita ce abin da jama'a suka samu a yau." "wannan burinmu ne, na bautawa kasarmu.”

Da yake magana bayan Netanyahu, Gantz ya ce ya zabi gwamnatin hadin kai, maimakon yakin basasa, ya kara da cewa lokacin "mummunan rikicin siyasar Isra'ila ya wuce."

Netanyahu ya yi alkawarin samar da kasafin kudin da “zai hana tattalin arzikin kasar durkushewa, da samar da daidaiton da zai maido da ci gaba."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG