Yanzu haka dai za a iya cewa an shiga kafar wando daya tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo, bayan da wata wasika da Obasanjo ya rubuta inda yake suka ga yadda Buhari ke gudanar mulkin ‘kasa, har ma yake cewa bai kamata ba shugaban ya sake neman wa’adin shugabanci na biyu ba.
Sai kuma cece-kucen da ya biyo bayan maganar yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari ke bi, wanda Obasanjo yake ganin ana nuna son kai da banbanci wajen aiwatar da shi.
Takon saka na baya-bayan nan da ya fito shine bayanin da shugaba Buhari ya yi na cewa zamanin gwamnatin Obasanjo an kashe zunzurutun kudaden dalar Amurka miliyan dubu 16, ba tare da an samar da wutar lantarkin da aka an kashe kudin domin samarwa.
Shi kuma Obasanjo ya mayar da martani inda yake cewa shugaba Buhari ya jahilci irin yadda gwamnati ke gudanar da ayyukanta, domin a baya an binciki wannan magana a Majalisar ‘kasa da kuma hukumar EFCC ba tare da angano komai ba.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.
Facebook Forum