Muryar Amurka ta zanta da wasu kananan ‘yan kasuwa da wasu magidanta a yankin kudu maso gabashin Najeriya. A cewar Mallam Mika’ilu Yaro wani karamin dan kasuwa, shigowar azumi yasa kayan masarufi sunyi tsada, da suka hada da Tumatir da Albasa da Attarihu, kuma gashi yanayin kasuwa babu kudi.
Itama wata ‘yar kasuwa mai suna Usilia Okeke, cewa ta yi lokacin da aka fara azumi farashin kayayyakin da suke sayarwa ya tashi, har ma ya ribanya kudin da suke sarowa a baya.
Alhaji Tijjani Umaru daga kasuwar Abakaliki, cewa duk wasu kayayakin masarufi da suke saya suna sayarwa a kasuwa farashinsu ya karu.
Sai dai mallam Rabi’u Isufu Bagobiri wani mai shago a tsohon garken garin Okigwe dake jihar Imo, ya ce har yanzu farashin wasu kayan marmari na nan a yadda suke basu canza ba.
Masu sharshi kan al’amura na ganin tashin farashin kayayyaki lokacin azumi yana da nasaba da rashin Imani da son zuciya, kasancewar wasu mutane na jiran samun dama irin ta wannan watan domin su kara kudin kayayyakinsu don neman riba mai yawa.
Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.
Facebook Forum