Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cassie Ta Maka Diddy A Kotu Kan Zargin Fyade, Cin Zarafi


Sean P. Diddy Combs, hagu, tare da Cassie Ventura, dama, a shekarar 2016 a Los Angeles
Sean P. Diddy Combs, hagu, tare da Cassie Ventura, dama, a shekarar 2016 a Los Angeles

Lauyan Combs ya musanta dukkan zarge-zargen wadanda ya kwatanta a matsayin “marasa kan gado.”

An maka fitaccen mawakin zamani na Amurka Sean Combs da ake kira P. Diddy a kotu kan zargin fyade da cin zarafin mawakiya Cassandra Ventura wacce aka fi sani da Cassie.

A wani lokaci a baya, Ventura ta kasance budurwar Diddy, ta kuma maka shi a kotu ne a ranar Alhamis a birnin New York.

A karar da ta shigar, Ventura ta zargi Diddy da tilasta mata shan miyagun kwayoyi, tare da yi mata duka kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.

Ta kara da cewa ya sha tilasta mata ta yi lalata da wasu maza masu zaman kansu.

A cewar karar da Ventura ta shigar, Diddy ya taba yi mata fyade a shekarar 2018 a lokacin da ta yi yunkurin rabuwa da shi.

Lauyan Combs, Ben Brafman, ya musanta dukkan zarge-zargen wadanda ya kwatanta a matsayin “marasa kan gado” da yunkurin “cin da ceto.”

Ventura mai shekaru 37 a yanzu, ta hadu da Combs ne mai shekaru 54 a shekarar 2005.

A lokacin da suka hadu, Diddy na da shekaru 37, ita kuma tana da shekaru 19.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG