Omah Lay ya yi fice ne wajen rera wakoki irin na "Afrobeat," ko da yake, a wata hira da tashar talbijin ta Channels ta yi da shi, ya ce ba shi da takamaiman salon waka.
Kafafen nishadi na Najeriya sun wayi garin a ranar Alhamis da labarin yadda Bieber da ke da mabiya miliyan 164 a shafinsa na Instagram, ya fara bin Omah Lay wanda ke da mabiya miliyan 1.1.
Ba dai kasafai ake samun shahararrun mawakan kasashen yammaci duniya suna bin takwarorinsu na sauran sassan duniya ba, musamman na Afirka.
Binciken da VOA Hausa ta yi, ya tabbatar da cewa Bieber, dan shekara 26 ya fara bin mawakin na Najeriya wanda asalin sunansa Stanley Omah Didia.
Hakazalika shi ma mawakin na Najeriyar ya fara bin Bieber.
Omah Lay, ya fito idon duniya ne da wakokinsa irinsu “Bad Influence,” “Lololo,” “Hello Brother,” “Godly,” da kuma “My Bebe.”
Dan shekara 23, Omay Lay haifaffen birnin Fatakwal ne da ke jihar Rivers a kudu maso kudancin Najeriya.
Ya kuma taba samun gayyatar mawaki Olamide a wakarsa ta “Infinity.”
A karshen makon da ya gabata ya samu lambar yabo a bikin Headies na karrama mawaka da aka yi a birnin Legas, inda aka karrama shi a matsayin “tauraron mawaki” mai tasowa.
Wata kamanceceniya da mawakan biyu (Omah Lay da Bieber) suke da ita, ita ce, tun suna da kananan shekaru suka fara fito da basirarsu ta iya waka.