Yanzu haka dai shugaba Magafuli shine shugaban Gabashin Africa na farko da ya taba daukar mace a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.
Domin ta ma Samia Suluhu Hasan ta dauki rantsuwar kama aikin gaban dubun dubatan al’umma na ciki da wajen kasar a babban birnin kasar wato Dares As’salam.
A cikin wata yar gajeruwar jawabi da sabon shugaban yayi ya jaddada wa yan kasan ne zai cika alkawurran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.
‘’Yace muna sane da da dinbin aikin dake gaban mu, na irin aikin da kuka bamu kuma da ikon ALLAH da taimakon ku, ku jamaa ina mai tabbatar muku cewa zamu kai ga gaci’’.
Kana Shugaba Magafuli ya roki yan kasan ta Tanzania da suci gaba da kasancewa tsintsiya madaurin ki daya, yace kowa mai nasara game da wannan zaben, musammam ganin yadda zaben aka kammala shi cikin lumana, don haka yace yanzu kasar ce a gaban mu.
Shugabannin Africa da dama ne dai suka halarci wannan bikn rantsarwar, ciki ko harda shugaban Rwanda Paul Kagame da Jacob Zuma na Africa ta kudu,da kuma shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe. Wannan zaben dai ya kara tsawon wa’adin jammiyyar CCM mai mulkin kasar, zaben da yan adawa suka sa kafa suka yi fatali dashi suka ce ba kome cikin sai magudi da son rai.