Mista Nkurunziza ya cinye kuri’un da kimanin kaso 69, a yayin da dan hamayyar da ya biyo bayansa ya tsira da kashi 19, inji shugaban zaben Pierre Claver Ndayicariye. Wannan ce ta bashi damar lika shi Agathon Rwasa da kasa.
AMurka dai da Birtaniya tuni suka yi tir da wannan zaben saboda rashin cancantar yinsa. Musamman ma yadda aka yi sharer fagen zaben da rikice-rikice tare da firgita ‘yan hamayya da kuma yadda jam’iyyun adawar suka koka da karya ka’idar da aka yi.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace, Nkurunziza ya fadi ba nauyi a wajen su musamman yadda yayi amfani da siyasar karfa-karfa don komawa mulki. A farko makon nan ne dai tsohon shugaban kasar Burundi Domicien Ndayizeye yayi kira ga kasashen duniya da su yi watsi da sakamakon zaben na Burundi.