Makasudin taron shi ne masu ruwa da tsaki a jihar su tattauna matsalar tsaro a jiharsu da a cikin 'yan kwanakin nan yayi sanadiyar rasa rayuka da dama da dukiyoyi masu dimbin yawa a sassa daban daban na jihar.
Alhaji Muhammed Abubakar Ahmadu sarkin yakin Lafiya shi ya karanta matsayin mahalarta taron. Yace taron ya umurci gwamna cewa duk shawarwari da aka ba gwamnatin bisa ga binciken tashin hankali da gwamnati ta sani to a yi anfani dasu a aiwatar da abun da suka ce domin abubuwan dake faruwa a jihar tamkar aikin 'yan ta'ada ne. A wurare kamar su Agyaragu, Asakyo da dai sauransu an kashe mutane da dama. Gwamnatin jiha ta dauki matakai kuma gwwmnatin tarayya ta taimaka. Mutanen da aka san sun karya doka a hukuntasu.
Wasu da aka gayyata taron kamar ministan yada labarai Labaran Maku da Sanata Solomon Ewuga mai wakiltar arewacin jihar Nasarawa da wasu 'yan majalisar dokokin jihar basu halarci taron ba.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar jihar Muhammed Baba Ibako ya bayyanawa wakiliyar Murya Amurka dalilinsu na kauracewa taron. Yace wanda ya kira taron wato gwamnan jihar sun nemi zama dashi kafin a yi zaben kananan hukumomi da 'yansanda da sauran masu ruwa da tsaki su zo majalisar dokokin jihar su tattauna. Gwamnan yaki. Yace duk abun da ya shafi harakar tsaro su bar masa. Yace masu nasu aikin yin dokoki ne kawai sabili da haka bai halarci taron ba. Yace gwamnan shi ne ya kawo rikici. Misali ya kira Fulani ya basu matsayi kana ya cire kudi ya basu. Kwana biyu bayan yayi hakan Fulani suka fara kashe mutane.
Shi ko sarkin Fulanin jihar Nasarawa Sanata Wali Jibril yace taron yayi tasiri. Ya zo taron ne sabili da jihar Nasrawa ne, saboda abubuwan dake damun jihar da kuma rashin mutanensa da yayi a jihar, saboda kashe mutane da aka yi a jihar. Yakamata ya kasance a wurin taron. Yace ba maganar jam'iyya ba ce. Magana ce ta tsaron jihar.
Sanata Wali Jibril ya bukaci a fadada taron domin mutane da yawa basu halarci taron ba. A bisu a san dalilin rashin zuwansu domin duk su hadu su yi maganar tsaron jihar Nasarawa.
Andona na Doma Abdullahi Aliyu Onawo shi ma ya bukaci al'umma ne da su yi hakuri su zauna lafiya. Yace hakin sarakuna ne su nemi zaman lafiya da cigaban al'ummarsu sabili da haka ya kira kowa yayi hakuri, a yafewa juna a zauna lafiya. Inda ake bukatar gyara sai a yi cikin lumana da hankali domin yin hakan shi ne zai kai ga biyan bukata ba bacin rai ba.
Tun farko sai da gwamnan jihar Tanko Umaru Al-Makura ya jajantawa wadanda suka yi rashi a tashe-tashen hankula da suka addabi jihar.
Ga rahoton Zainab Babaji.