Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Sake Tafiya London Don Duba Lafiyarsa


hugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
hugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Shugaban zai dawo cikin mako na biyu a watan Yuli kamar yadda wata sanarwa da fadarsa ta fitar a ranar Alhamis.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi London a ranar Juma’a don duba lafiyarsa, fadar gwamnatin kasar ta bayyana.

Buhari zai tafi London da ke kasar Birtaniya a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni 2021, don komawa ya sake bibiyar lafiyarsa.” Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta ce.

Shugaban zai dawo a mako na biyu cikin watan Yulin da ke tafe a cewar Adesina.

A watan Maris Buhari ya kai ziyara birnin na London inda ya je duba lafiyarsa, ya kuma kwashe kusan mako biyu a can kafin ya koma gida.

Wannan ita ce ziyara ta biyu cikin wata kusan uku da shugaban zai je London don ganin likita.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, Birtaniya, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG