Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Koma Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Komawar ta shugaba Buhari Najeriya, na zuwa ne yayin da mutane suka fara dasa alamar tambaya kan yaushe zai koma gida.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya, bayan sama da makonni biyu da ya kwashe a birnin London ana duba lafiyarsa.

Bashir Ahmad, wanda ke ba Buhari shawara kan harkar kafafen sada zumunta na zamani ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter dauke da hotunan shugaban a lokacin da ya sauka filin jirgi.

“Shugaban Najeriya ya isa Abuja da tsakar rana, bayan wata tafiya da ya yi zuwa London da ke Ingila.” Bashir ya wallafa a shafinsa @Bashiraahmad.

A ranar 30 ga watan Maris shugaban kasar ya kama hanyarsa ya bar Najeriyar, inda cikin wata sanarwar da fadarsa ta, aka bayyana cewa zai koma kasar a tsakiyar watan Afrilu.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Tafiyar tasa ta taso a daidai lokacin da likitcon Najeriya ke shirin yajin aiki, lamarin da ya kara zafafa muhawarar da aka yi ta yi kan zuwansa London.

Bangaren adawa da wasu ‘yan Najeriya sun soki ziyarar ta suna masu cewa kamata ya yi a inganta fannin kiwon lafiyar kasar ta yadda ba sai shugabanni sun fita kasashen ketare ba.

Fadar shugaban kasar ta mayar da martani inda ta ce, dama shugaban ya saba yin irin wannan tafiya tun kan ma ya zama shugaban kasa, “saboda haka ba bakon lamari ne ba ne,” in ji kakakin Buhari Garba Shehu.

Tafiyar har ila yau ta tattago batun rashin mikawa mataimakinsa Prof. Yemi Osinbanjo ragar mulkin kula da kasar, abin da fadar ta shugaban kasa ta ce, doka ta ce sai idan shugaban zai haura kwana 21 kafin ya mika mulkin.

Amma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce, Buharin ya ki ba Osinbajo mulki ne saboda yana gudun kada ya fi shi tabuka abin a-zo-a-gani.

A makon farko da ya isa London, wasu ‘yan Najeriya mazauna birnin sun yi zanga-zangar nuna adawa ga shugaba a kofar gidan da ya sauka, inda kwana daya bayan hakan, wasu magoya bayan Buharin suka yi tasu zanga-zangar ta nuna masa goyon baya.

XS
SM
MD
LG