A ranar Alhamis Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Yayin wannan ziyara ta kwana guda, dakarun kasar za su gabatarwa da shugaban kasar rahotonni kan yakin da suke yi da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriyar kamar yadda daya daga cikin hadimansa Bashir Ahmad ya bayyana.
Kazalika Buhari zai kaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar Farfsesa Babagana Umara Zulum ya yi.
A watan Yuni, shugaban kasar ya kai ziyara a jihar inda a wancan lokaci ma ya gana da dakarun kasar tare da kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.
Daga cikin ayyukan da ya kaddamar akwai rukunin gidaje 10,000 da gwamnatin tarayya ta dauki nauyin ginawa don samar da matsugunai ga ‘yan gudun hijira.
Jihar Borno ta kasance cikin kangin hare-haren mayakan Boko Haram lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ya kuma raba wasu miliyoyi da muhallansu.