Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Sallami Ministoci Biyu


Tsohon Ministan noma Mohammed Nanono da aka sallama (Facebook/Fadar gwamnatin tarayya)
Tsohon Ministan noma Mohammed Nanono da aka sallama (Facebook/Fadar gwamnatin tarayya)

Kakakin shugaba  Buhari Femi Adesina ya tabbatar da sallamar ministocin biyu wadanda tuni an maye gurbinsu da wasu.

Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kori wasu ministocinsa biyu.

Ministocin sun hada da Ministan noma Mohammed Nanono da ministan kula da bangaren lantarki Saleh Mamman.

Kakakin shugaba Buhari Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Tuni an maye gurnin ministocin biyu a cewar Adesina, inda ya kara da cewa Dr. Mohammed Mahmood Abubakar wanda shi ne ministan muhalli ya maye gurbin Nanono yayin da Eng. Abubakar D. Aliyu wanda shi ne ministan ayyuka ya maye gurbin Mamman.

Tsohon ministan wutar lantarki Saleh Mamman (Facebook/Saleh Mamman)
Tsohon ministan wutar lantarki Saleh Mamman (Facebook/Saleh Mamman)

Buhari ya ce wannan garanbawul da aka yi, na da alaka da tsarin da aka saba bi na yin nazari kan yadda aka aiwatar da ayyuka ta hanyar gabatar da rahoto wadannan ayyuka a taron majalisar.

“Wannan muhimmin mataki na garanbawul da aka dauka, sun taimaka wajen gano wuraren da ake da rauni da kuma karfi, da kuma rufe gibin da ake da shi a sha’anin gudanar da gwamnati, sarrafa tattalin arziki da kuma biyawa ‘yan Najeriya bukata.” In ji Adesina.

“Na gana da minsitocin da za su tafi don mika godiya kan irin gudunmowar da suka bayar. Yau ita ce rana ta karshe da za su halarci taron majalisar zartawa na tarayya, ina kuma masu fatan alheri kan al’amuran da suka a gaba.” Buhari ya ce a jawabinsa a talon majalisar.

Majalisar zartarwar ta gudanar da taronta na mako-mako a fadar ta shugaban kasa wanda shi ne na farko a wannan sabon wata.

XS
SM
MD
LG