Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Sallami Darektan Hukumar NAPTIP


Basheer Garba Mohammed (Facebook/NAPTIP)
Basheer Garba Mohammed (Facebook/NAPTIP)

Sallamar Mohammed na zuwa ne kasa da wata hudu bayan da aka nada shi a mukamin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sallami Basheer Garba Mohammed, Darekta-Janar na hukumar yaki da bautarwa da fataucin dan adam ta NAPTIP.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya ce an maye gurbin Mohammed da Fatima Waziri- Azi.

Sai dai sanarwara ba ta ambaci dalilin cire Mohammed a wannan mukami nasa ba.

Amma ta ce, Ministar jin-kai da kare aukuwar bala’i Sadiya Umar Farouq ce ta ba da shawara a Waziri-Azi shugabancin hukumar.

Cikin sanarwar Shehu ya ce ministar ta nuna bukatar a gaggauta karfafa ayyukan hukumar domin ta samu ta cimma burinta.

“An zabi Fatima Waziri-Azi saboda irin kwarewa da take da shi wanda zai iya ciyar da hukumar gaba ta hanyar dorawa kan ayyukan da aka faro.” Shehu ya ce.

Sallamar Mohammed na zuwa ne kasa da wata hudu bayan da aka nada shi a mukamin.

A ranar 27 ga watan Mayun 2021, aka nada shi a matsayin shugaban hukumar ta NAPTIP, inda ya maye gurbin Mrs. Imaan Suleman Ibrahim.

Sallamar Mohammed na zuwa ne, makon guda bayan da Buhari ya sauke ministan noma Muhammed Sabo Nanono da ministan wutar lantarki Saleh Mamman.

Fatima Waziri-Azi ita ce tsohuwar jami’a mai kula da sashen dokokin da suka shafi al’uma a cibiyar nazarin ilimin shari’a.

Ta kuma kasance mai kare hakkin mata kan abubuwan da suka shafi cin zarafin da muzgunawa a tsari na zamantakewa.

XS
SM
MD
LG