Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Sake Jaddada Kalaman Da Kamfanin Twitter Ya Goge


Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)
Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)

“Kamar yadda na fada a baya, za mu dauki mataki akansu daidai da irin yaren da suka fi fahimta.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake nanata matsayarsa da ya bayyana a baya, ta cewa zai yi maganin masu ta da kayar baya a kudu maso gabashin kasar “da irin yaren da suka fi fahimta.”

Buhari na nuni ne da irin tsauraran matakan da jami’an tsaron kasar ke shirin dauka akan mayakan kungiyar IPOB da ke fafutukar ballewa daga Najeriyar.

“Kamar yadda na fada a baya, za mu dauki mataki akansu daidai da irin yaren da suka fi fahimta.” Shugaban na Najeriya ya fada yayin wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Arise TV a Legas.

Wadannan kalamai shugaban ya wallafa a shafin Twitter a makon da ya gabata, lamarin da ya sa kamfanin ya goge sakonsa.

A wani abu da ake ganin martani ne, hukumomin Najeriya sun haramta amfani da kafar.

“Mun ba ‘yan sanda da sojoji umarnin su dauki tsauraran matakai akansu, kuma ku tsaya ku gani, nan da wasu ‘yan makonni za ku ga canji.” Shugaban ya kara da cewa.

Buhari ya ce sun ba manyan hafsoshin tsaron kasar dama su zagaya sassan kasar don su ga yadda matsaloli tsaron suke.

“Za su tabbatar da cewa sun maido da zaman lafiya, ba ma so mu ta yayata shirin da muke yi ne, gudun kada mu ankarar da miyagu.”

Sai dai a wannan karon ya hada har da ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a arewa maso yammaci.

“Idan ba mu dauki wannan mataki ba, mutane ba za su iya zuwa gonakinsu ba, hakan kuma zai haifar da matsalar yunwa.” In ji Buhari.

Ya kuma kara da cewa, ya samu tabbaci daga wasu Dattawa da matasan yankin kudu maso kudancin kasar cewa, suna goyon bayan zaman Najeriya a matsayin kasa guda.

“IPOB wani dan dugo ne a wani babban kewaye, ba bu inda za su iya zuwa, ina ga IPOB ba sa tunani idan ka yi la’akkari da yadda suke a ko ina a sassan kasar ta fannin kasuwanci da mallakar kadarori.”

Yayin wannan hira, Buhari ya tabo batutuwa da suka shafi, ilimi, nade-naden mukamai a gwamnatinsa da sauran batutuwa da suka shafi kasar.

Buhari ya kai ziyara jihar ta Legas ne a ranar Alhamis, inda ya je kaddamar da wasu ayyuka ciki har da bude tashar hanyar dogo da aka kammala wacce za ta rika tashi daga Legas zuwa Ibadan.

XS
SM
MD
LG