Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin mai adadin Naira Tiriliyon 7.2, ya kuma kasafta kudin da cewa kashi 30.7 zasu tafi a manyan ayyuka irin na ma’aikatun da suka hada da: ma’aikatar tsaro da ma’aikatar Ilimi da ma’aikatar cikin gida da ma’aikatar kiwon lafiya da dai sauransu.
Ana gina kasafin kasafin kudin Najeriya bisa kudin gangar ‘danyan Man fetur a kasuwar duniya, sai kuma cin basussuka daga waje da kuma cikin gida. Cikin kudin kasafin da shugaba Buhari ya gabatar Tiriliyon 7.2, za a ciwo bashin Naira Biliyan 429 domin yin ayyuka.
Lakabin kasafin kudin bana shine ‘kasafin kudin bunkasa tattalin arziki’ wanda ke nufin kasafine da zai fitar da Najeriya daga kangin talauci da rashi da kuma farfado da tattalin arzikin kasar na din din din.