Kungiyar malaman tace daga cikin shirin da tayi na bude karamin bankin kasuwanci a jahar Neja, ta sami damar baiwa malaman bashi.
Sakataren kungiyar malaman a jahar Neja, kwamarad Labaran Garba, yace bisa la’akari da halin rashin biyan albashi akan kari yasa suka dauki matakin baiwa malaman bashi.
A halin da ake ciki dai kungiyar malaman tace ta sami ribar Naira Miliyan 85 a sakamakon bude karamin bankin kasuwancin da Naira Miliyan 100 a cikin kimanin shekaru hudu da suka gabata, a cewar shugaban daraktocin bankin na NUT mallam Muhammad Sadauki.
Kungiyar ta gudanar da babban taronta na shekara domin bayyana irin ci gaba da aka samu sakamanon bude karamin bankin kasuwanci. Haka kuma wasu daga cikin malaman karantun sun nuna jin dadinsu da gamsuwa da wannan banki da kungiyar NUT ta bude.
Domin karin bayani.