Jaridar ta ce wata majiyar tsaro ta tsegunta mata cewa kimanin Hafsoshi da sojoji dari da daya ne suka arce daga filin biyo bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai a Marte da Dikwa.
Jaridar dai ta wallafa sunayen sojojin da tace sun tsere daya bayan daya.
Amma a martanin da ta mayar, shelkwatar sojojin Najeriya ta ce sam ko kadan wannan labari ba gaskiya ba ne.
Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar MM Yerima, ya fadi cewa bisa ga yanayi na yaki, bayan kammala gumurzu ana kidayar dakaru da kayan aikin da aka yi amfani da su, wurin tattara bayanai ne aka samu akasi amma daga bisani duk sojojin da ake magana akan su sun koma rundunoninsu.
A halin yanzu ma ana ci gaba da kai farmaki a filin daga da sojojin, a cewar Yerima.
To amma masana harkokin tsaro sun sami banbancin ra'ayi kan abinda ya faru. Dr. Yahuza Ahmed Getso, ya ce lallai kam in an ce dakarun sun gudu to abu ne mai yiwuwa duba da halin da ake ciki a yankin.
Shi ko mai bincike kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi Dr. Kabiru Adamu cewa ya yi ba lallai ba ne ace sojojin sun gudu, amma suna iya janyewa a irin dabarar nan ta yaki daga bisani kuma su koma. Ya na mai zargin 'yan jarida da nuna rashin kishin kasa wajen bada irin wannan rahoto.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina.