Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boris Johnson Ya Yiwa Miliyoyin 'Yan Hong Kong Tayin Zama ‘Yan Britaniya


Prime Ministan Britaniya Boris Johnson a yau Laraba, ya yi tayin baiwa miliyoyin mazauna birnin Hong Kong damar kasancewa ‘yan kasar Britaniya, idan kasar China ta kakaba dokar tsaro ta kasa da ‘yan adawa ke fargabar za ta kawar da ‘yancin siyasa a yankin.

Majalisar dokokin China ta amince da wani kudurin doka a makon da ya gabata, da ya bada damar girge jami’an tsaro a Hong Kong a karon farko, wanda manazarta ke ganin zai share fagen kuntatawa ‘yan adawa.

An amince da kudurin dokar ne domin martani ga jerin zanga-zangar neman kafa dimokaradiyya a Hong Kong.

Prime Minista Johnson ya wallafa a wata sanarwa cewa, “Idan har China ta ci gaba da kafa dokar bisa fargabar da take yi, to kuwa Britaniya ba za ta zura ido haka kawai ba; a maimakon haka, za mu yi irin na mu karimci mu kuma samar da wani zabin”.

Johnson ya jaddada kudurin kasar ta Britania, na baiwa dukkan mazauna Hong Kong da ke da passpo na kasar Britania damar zama ‘yan Britaniya, su kuma koma da zama a can.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG