Bola Tinibun yace ya kai ziyara jihar ne sakamakon yawan labaran da suka dade suna ji ta kafofin labarai na kisan jama’a da yin garkuwa da mutane dama, satar dukiya, da shanu, domin jajantawa Al’ummar, ya kara da cewa lamarin abin takaici ne.
Gwaman jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello ya yabawa Tinibu inda ya ce matsalar rashin tsaro ba karamar matsala bace a jihar, ya kara da bada bayanin yadda kwanakin baya ya ziayarci garuruwan da ‘yan bindiga suka kulle masu ibada a masallaci suka bude wuta a kansu.
Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce suna goyon bayan Tinibun a zabe mai zuwa domin ganin Najeriya ta samu irin moriyar dimukurayya da jihar Lagos ta samu alokacin da yake Gwamna.
Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagos, wanda ya nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a baya, ya bayyana niyarsa ta neman jam'iyarsa ta APC ta tsaida shi takarar shugaban kasa, kamar yadda ya bayyana a ziyarar da ya kaiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kwanan nan.
Ra'ayin 'yan jam'iyar musamman a yankin da Tinubu ya fito sun banbanta dangane da batun inda wadandansu suke goyon bayansa, yayinda wadansu suka gwamnace tsohon dan gidanshi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo wanda shime ya bayyana niyarsa ta tsayawa takara.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: