Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Yi Sabon Shugaba


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji.
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji.

Kungiyar Boko Haram ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abubakar Shekau, ta hanyar wani hoton bidiyo da ke nuna sabon shugaban kungiyar, wanda ya sha alwashin daukar fansa akan kisan da aka yi wa shugaban na su.

A cikin sakon bidiyon da aka yi a harshen Larabci, an nuna sabon kwamandan kungiyar ta Boko Haram, Bakura Modu, wanda aka fi sani da Sahaba, yana jawabi, tare da kira ga kwamandodin kungiyar da su ci gaba da dagewa da biyayya, duk kuwa da mutuwar shugaban na su da ya ce “yayi mutuwar shahada.”

Wata majiya da ke kusa da kungiyar ta Boko Haram ce ta samarwa kamfanin dillancin labarai na AFP hoton bidiyon, a yayin da wata majiyar ta daban kuma ta tabbatar da cewa sabon shugaban Bakura Modu ne ke jawabi a bidiyon.

A cikin bidiyon, Bakura yana zagaye ne da wasu mayakan kungiyar a bayansa, kamar yadda kungiyar ta al’adanta a duk lokacin da za ta ba da sako irin wannan.

Ya bukaci kwamandodin kungiyar ta 'Jama’atu Ahlus Sunna Lidda’awati Wal Jihad' da ka da su bari abin da ya faru ya raunata musu gwiwa "wajen fuskantar jihadi da abokan gaba."

Haka kuma yayi kira gare su da su yi watsi da shugaban ISWAP Abu Musa Al-Barnawi, inda ya jaddada cewa za su ci gaba da yaki da ISWAP din, har ma da daukar fansa.

Karin bayani akan: Abubakar Shekau, Abu Musa Al-Barnawi, jihar Borno, ISIS, ISWAP, UNHCR, Boko Haram, Bakura Modu, Nigeria, da Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa Shekau, wanda sunan sa ya dada shahara bayan sace daliban makaranta 300 a shekarar 2014, ya kashe kan sa a watan da ya gabata, a maimakon mika wuya ga bangaren ISWAP da ke adawa da Boko Haram, wadda ta kai masa hari a sansanin sa da ke dajin Sambisa a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

A cikin wani sakon murya, Shugaban ISWAP Abu Musa Al-Barnawi, ya tabbatar da cewa Shekau ya kashe kan sa, a yayin fafatawar.

Tun bayan mutuwar ta Shekau kuma, ISWAP din ta shiga farautar kwamandodin Boko Haram da suka ki mika wuya gare ta.

Kungiyoyin biyu dai sun raba gari ne a shekarar 2016, sa’adda ISWAP din ta soma kalubalantar matakin Abubakar Shekau na kai hari akan farar hula musulmai da basu ji ba ba su gani ba ba tare da tantancewa ba, da kuma yin amfani da mata domin harin kunar bakin wake.

Wasu rahotannin kuma na ta’allaka baraka a kungiyar ne da tsarin da Abubakar Shekau ya bi wajen amfani da wasu miliyoyin kudade da kungiyar ta samu na tallafi daga ISIS, inda wasu daga cikin shugabannin suka zarge shi da kokarin yin zalunci.

Fiye da mutane 40,000 ne dai suka mutu, a yayin da wasu miliyan 2 suka bar gidajensu sakamakon hare-haren kungiyar ta Boko Haram, tun somawar ayukan ta a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekarar 2009.

Wata Kungiya Mai Alaka Da IS Ta ce Shugaban Boko Haram Shekau Ya Mutu

Wata Kungiya Mai Alaka Da IS Ta ce Shugaban Boko Haram Shekau Ya Mutu
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00

XS
SM
MD
LG