WASHINGTON, D.C. —
A maimakon haka, majalisar ta ba wa gwamnati umurnin aiwatar da shawarwari da ke kunshe a wani rahoto da Majalisar ta kaddamar akan tsaron Kasar.
Wanan mataki da Majalisar dattawa ta dauka, ya biyo bayan wasu kudurori ne guda biyu wadanda Sanata Abubakar Kyari Mai wakiltan Jihar Borno ta Arewa, da Sanata Bello Mandiya mai wakiltan Katsina ta Kudu suka kawo akan tabarbarewar sha'anin tsaro a mazabun su.
A gudumawa daban daban da Sanatocin suka bayar, sun nuna damuwa sosai da Allawadai da kashe kashe da rasa rayuka da kuma sace sacen mutane da ke aukuwa a fadin kasar da kuma abinda suke ganin gazawa ta hukumomin tsaro wajen magance matsalolin.
Sanata Abubakar Kyari Mai wakiltan Borno ta Arewa a Majalisar Dattawa ya koka akan wani hari da Yan Boko Haram suka kai sansanin yan gudun hijira a Tumur ta Jihar Difa a jumhuriyar Nijer.
Ya ce wanan sansani na da yan Najeriya sama da dubu arba'in, an kashe Sama da Mutane 30 a lokaci guda, sannan kuma an kona matsugunan nasu, Sanata Kyari ya ce dole a chanja Salon tsaro a kasa. Sanata Kyari ya ce a matsayin su na wakilan jama'a ba za su daina magana akan rashin tsaro ba har sai sun ga andauki mataki kwakwara.
A lokacin da Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Katsina, Bello Mandiya ke bayanin sa, ya jaddada muhimmacin nauyin da kundin tsarin mulkin Kasa sashi na 14 ya dorawa gwamnati, wato bada tsaro ga al'ummomin ta, amma yana ganin sai mahukunta sun tashi tsaye sosai domin a kubutar da daliban da aka sace a mazabar sa, saboda gudun kar a maimaita abinda ya faru da 'yan matan Chibok da Dapchi.
Majalisar ta bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya duba lamarin, sannan ya gaggauta aiwatar da shawarwarin da kwamitin Majalisar Kan matsalolin tsaro Suka bayar, da ya kunshi hukuncin da majalisar ta yanke a matsayin hanyoyin magance matsalolin tsaro a fadin kasar.
Batutuwan sha'anin tsaron nan dai shi ne a yanzu yafi daukan hankalin mafi yawan al'umomi a cikin Kasar.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda cikin sauti