A ranar Litinin, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurkan Ned Price ya ce, a lokacin tattaunawar, Blinken ya zayyana irin yadda Amurka ke kallon dangantakar kasashen biyu bisa wasu muhimman batutuwa da suke mutuntawa kamar dimokradiyya, kare hakkin bil adama, da kuma dangantaka ta tsakanin juna da juna.
Blinken ya kuma yaba da nadin sabbin manyan hafsan sojojin kasar da shugaba Buhari ya yi don sauya irin yadda ake tunkarar ayyukan ta’addanci a arewa maso gabashi da tabbagtar da tsaro a sauran daukacin yankunan kasar.
Sakataren harkokin wajen na Amurka, ya yi nuni da yadda shugaba Biden ya soke takunkumi da aka sakawa Najeriya kan tsarin ba da visa, a matsayin wani mataki na nuna irin kusanci da ke tsakanin Amurkawa da ‘yan Najeriya.
Sannan ya jaddada goyon bayan Amurka ga Dr. Ngozi Okonjo Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO.
A farkon shekarar 2020 tsohon shugaba Donald Trump ya saka takunkumin visa akan Najeriya a sabon jerin sunayen kasashen da ya fitar wadanda aka hana su shiga kasar.
Amma bayan hawansa karagar mulki, shugaba Biden ya soke wannan doka da Trump ya saka.
Baya ga haka, gwamnatin Trump ta ki ba Najeriya goyon bayan a zaben shugaban kungiyar kasuwanci ta WTO inda ta gwammace ta goyawa ‘yar Korea ta Kudu baya.
Sai dai bayan hawan Biden mulki, ya sauya akalar tafiyar inda ya nuna goyon baya ga Najeriya kuma tuni har Dr. Okonjo-Iweala ta kama aiki a ranar 1 ga watan nan na Maris bayan da Amurka wacce ita kadai ta rage ta yi na’am da zabin Okonjo-Iweala.