Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya: Theresa May Ta Kalubalanci Jeremy Da Suyi Muhawara


Theresa May Da Jeremy Corbyn
Theresa May Da Jeremy Corbyn

A jiya Lahadi kasar Birtaniya da Kungiyar tarayyar Turai suka saka hannu akan yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga Kungiyar, bayan shafe shekaru biyu suna tattaunawa akan bukatar kasar.

Wani mai magana da yawun jam’iyar Labour ta kasar Birtaniya ya fada cewa shugaban jam’iyar Jeremy Corbyn, zai so suyi muhawara gaba da gaba tare da firaminista Theresa May, akan kokarinta na ganin an amince da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai da kuma makomar kasar gaba daya.

Firaminista Theresa May, ta bada shawara a wata hira da tayi da jaridar 'The Daily Telegraph' tana da sha’awar ta kalubalanci Corbyn, da suyi muhawara a talabijin akan ficewar kasar Birtaniya, daga tarayyar turai yayin da ta kaddamar da kamfe din ta na neman amincewa da yarjejeniyar ta hanyar 'yan majalisar kasar.

Mintoci arba’in kacal ya dauki May da sauran Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai suka saka hannu akan amincewa da yarjejeniyar fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai, bayan shekaru biyu da suka shafe suna shawarwari.

Sai dai har yanzu akwai kalubale dake tattare da kokarin samun amincewar masu ruwa da tsaki na Birtaniya game da yarjejeniyar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG